'Tinubu Ya Yi Watsi da Mu Bayan Zaben 2023', Shugabannin Mata Na APC Sun Koka - Legit.ng
'Tinubu Ya Yi Watsi da Mu Bayan Zaben 2023', Shugabannin Mata Na APC Sun Koka

'Tinubu Ya Yi Watsi da Mu Bayan Zaben 2023', Shugabannin Mata Na APC Sun Koka

  • Kungiyar shugabannin mata na jam’iyyar APC na jihohi 37 sun koka kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya ware su a rabon mukaman siyasa
  • Shugabar kungiyar, Patricia Yakubu, ta ce abin takaici ne yadda Tinubu ya ki tunawa da su duk da irin fadi tashin da suka yi a zaben 2023
  • Da ya ke mayar da martani, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya ba matan tabbacin cewa nan gaba kadan za a waiwaye su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mambobin kungiyar shugabannin mata na jam’iyyar APC sun ce Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da su bayan ya lashe zaben 2023.

Kara karanta wannan

"Buhun shinkafa da atamfa kawai aka raba mana bayan zabe," shugabannin matan APC

Shugabannin mata na APC sun koka da gwamnatin Tinubu
Shugabannin mata na APC sun zargi Shugaba Bola Tinubu da yin watsi da su bayan zaben 2023. Hoto: @iyalojasgeneral
Asali: Twitter

"Tinubu ya manta da mu" - Matan APC

Mambobin kungiyar, sun hada da shugabannin mata na jam’iyyar APC na jihohi 36 da babban birnin tarayya (FCT), jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana rashin jin dadin su ne yayin da suka kai wa Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar na kasa ziyara a Abuja, a ranar Talata.

Shugabar kungiyar, Patricia Yakubu, ta ce abin takaici ne yadda Tinubu ya ki tunawa da ko da mace daya daga cikinsu a yayin rabon mukamai.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Patricia Yakubu ta ce suna son a rika damawa da su a harkokin mata a kasar a matsayin ladar wahalar da suka sha a yakin zaben 2023.

"Ba a ba mu tallafi" - Matan APC

A cewar shugabar kungiyar:

“Tun bayan zaben 2023, buhun shinkafa daya da turmin zani daya kacal aka rabawa shugabannin mata na jihohi daga sakatariyar jam’iyyar ta kasa.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa Tinubu bai saka baki kan dambarwar Ganduje ba", APC ta magantu

“Babu wani abu da aka ba mu a lokacin Ista, Ramadan da bukukuwan Sallah. Hatta kayan abinci da aka raba ba su zo hannun shugabannin mata ba.
"Mai girma shugaban jam'iyya, cikin girmamawa, muna so mu sanar da kai cewa shugabannin mata sun sadaukar da komai na su wajen samun nasarar babbar jam'iyyarmu a zaben 2023."

Shugaban APC, Ganduje, ya yi martani

Da yake mayar da martani, Ganduje ya ce ana kan kokarin ganin an saka matan jam’iyyar APC a harkokin siyasar jam’iyya da gudanar da mulki, in ji rahoton jaridar The Punch.

"Ina so in yaba da gudunmawar da kuka bayar a lokacin zaben 2023 wanda ya kai ga gagarumar nasarar da babbar jam'iyyarmu ta samu."
“Zan ba ku tabbacin cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana sane da gudunmawar da ku ka bayar. Kuma akwai nade-nade da za ayi nan gaba, komai ana yinsa daki-daki."

Kara karanta wannan

Ba a gama da dambarwar Ganduje ba, an sake korar shugaban APC a Zamfara

-Abdullahi Ganduje.

'Yan majalisar YPP sun koma Labour

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa Hon. Iheanacho Nwogu da Hon. Fyne Ahuama, 'yan majalisar dokoki a jihar Abia, sun sauya sheka daga jam'iyyar YPP zuwa Labour.

Nwogu da Ahuama sun yi alkawarin marawa gwamnatin Alex Otti baya tare da yakinin cewa jam'iyyar LP ta kafu kan adalci kamar yadda suka fada a wasikar murabus din su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel