Waiwaye: Ƙona masallata a jihar Kano da yunƙurin haɗewar Atiku da Obi

Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Adadin mutanen da suka mutu a harin masallacin Kano ya kai 15

Masallacin da aka kona motane

A makon da ya gabata ne aka samu wani mummunan lamari a garin Larabar Abasawa da ke karamar hukumar Gezawa a jihar Kano inda wani matashi ya cinna wa wani masallaci wuta ana tsaka da sallar asuba.

Hukumomi a jihar da ke arewacin Najeriya sun ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar ya kai 15.

Wasu daga cikin wadanda suka jikkata a lamarin na kwance a asibiti, inda ake musu magani.

A ranar Laraba da asuba ne matashin ya cinna wa masallacin wuta bayan ya yayyafa wa masallacin fetur tare da kulle duka ƙofofin masallacin.

Majalisar Dattawa na so a bai wa ƙananan hukumomi ƴancin kai

Majalisar Dattawan Najeriya

Asalin hoton, NIGERIA SENATE

A cikin makon da ke karewa ne Majalisar Dattawan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda suka ce hakan zai iya magance matsalar tsaro da ake fama da ita da tururuwar da mutane ke yi zuwa birane da kuma rashin aikin yi.

Sanata Abdurrahaman Kawu Sumaila ne ya gabatar da kudurin wanda ya ce akwai bukatar a zauna da gwamnoni da masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a yi kananan hukumomi su samu ‘yancinsu da suka rasa a baya.

Kawu Sumaila ya ce a wannan lokacin za a samu nasara saboda salon da majalisar ta dauka a wannan karon ya sha bamban da matakan da aka rika dauka a baya.

Sanatan ya ce sun nemi shugaban kasa ya shige gaba wajen tabbatar da an samu abinda ake so, ta hanyar kiran taron masu ruwa da tsaki da zai kunshi gwamnoni da 'yan majalisu na tarayya da na jihohi da shugabannin al'umma da malaman addini da sauransu domin a tattauna domin samar wa kananan hukumomi matsaya guda.

Abin da ya sa muke ƙoƙarin haɗewa da Obi - Atiku Abubakar

Peter Obi da Atiku Abubakar

Asalin hoton, ATIKU ABUBAKAR/X

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce sun yi nisa wajen tattaunawa da sauran 'yan hamayya a fadin kasar domin ganin yadda za su kwace mulki a hannun jam'iyyar APC a nan gaba.

Atiku, wanda ya yi wa jam'iyyar PDP takarar shugabancin kasa a zaben 2023, ya bayyana hakan ne bayan wata ziyara da dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar Labour a 2023, Peter Obi, ya kai masa a cikin makon da ya kare.

Ya ce, " Ga duk wanda yake gani za a samu wani rikici tsakanina da Obi to babu abin da zai faru ko kadan, kuma mu a nan gaba kowa aka dauko don ya yi takara in dai ya cancanta za mu goyi bayansa."

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, ya ce," Ai a baya na fada cewa idan jam'iyyarmu za mu hadu a ce a bar wa mutumin da ya fito daga Kudu maso Gabas za mu yarda."

Shugaba Tinubu ya buƙaci hukumomi su koma amfani da motoci masu amfani da iskar gas

Shugaba Bola Tinubu

Asalin hoton, Getty Images

Shugaba Bola Tinubu ya umarci duka hukumomin gwamnati da su sayi motoci masu amfani da iskar gas a wani ɓangare na yunƙurin da ƙasar ke yi na komawa amfani da makamashi maras gurɓata muhalli tare da rage tsadar mai.

Umarnin na ƙunshe ne cikin sanarwar da kakakinsa, Ajuri Ngelale ya fitar inda sanarwar ta ce, Tinubu ya ce yana sa ran duka hukumomin gwamnati da ma'aikatu su soma rabuwa da motocin da suke da su masu amfani man fetur ko dizel.

Shugaban ya ƙara da cewa duk sababbin motocin gwamnati ko babura masu ƙafa uku dole ne su yi amfani da nau'in iskar gas na CNG da hasken rana ko ta hanyoyin makamashi.

Shugaban ya kuma bayyana ƙudirinsa na amfani da iskar gas yadda ya kamata domin magance tsadar sufuri ga al'umma.

Umarnin shugaban ya zo ne ƴan makonni bayan da gwamnati ta sanar da ƙudirinta na samar da motocin bas da babura masu ƙafa uku fiye da 2,000 masu amfani da iskar gas a ƙoƙarin rage tsadar sufuri kafin 29 ga watan Mayu, lokacin da shugaban zai cika shekara ɗaya a karagar mulki.

EFCC za ta gurfanar da Emefiele kan sabunta takardun naira

Godwin Emefiele

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya ta'annati, EFCC ta ce za ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele a gaban kotu bisa bayar da izinin buga sababbin takardun naira na miliyan 684.5 a kan naira biliyan 18.96.

Tun farko an tsara gurfanar da shi ne ranar 30 ga watan Afirilu da ya gabata amma aka ɗage ranar bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kotun da kuma ɓangarorin shari'ar.

A tuhume-tuhumen huɗu da aka shigar a kansa, EFCC ta yi zargin Emefiele ya yi burus da umarnin kotu da nufin jefa jama'a cikin mawuyacin hali lokacin aiwatar da tsarin sauya takardun naira da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi.

EFCC ta kuma zargi Emefiele da bayar da izinin cirar naira biliyan 124.9 daga asusun bai ɗaya na ajiyar kuɗaɗen gwamnati ba bisa ƙa'ida ba.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa tsohon gwamnan na CBN zai gurfana a gaban kotu kan waɗannan tuhume-tuhume gaban mai shari'a Maryann Anenih ta babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Laraba.